Wani Magidanci ya watsa ma Uwargidarsa tafasashshen talge, ko me ya yi zafi?

Wani Magidanci ya watsa ma Uwargidarsa tafasashshen talge, ko me ya yi zafi?

Wani Magidanci mai suna Bawa Joshua ya gurfana a gaban wata Kotun Majistri dake zamanta a garin Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, inda ake tuhumarsa da laifin kokarin hallaka matarsa Grace, ta hanyar watsa mata tafasashshen talgen tuwo.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, Sufeta Johnson Okunade ya bayyana ma Kotun cewar Bawa ya tafka wannan aika aika ne a ranar 7 ga watan Mayu da misalin karfe 8 na yamma a gidansu dake titin Ayoomodara, jihar Ekiti.

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Maigidan ya hau dokin zuciya ne sakamakon wata yar rikici da ta taso tsakaninsa da uwargidar tasa, daga nan kawai sai ya rarumi tunkunyar tuwo dake kan wuta ya juye ma mata talgen a jikinta, wanda ya kokkona mata jiki.

Wani Magidanci ya watsa ma Uwargidarsa tafasashshen talge, ko me ya yi zafi?
Tafasashshen talge

Dansandan ya kara da cewa laifin da Bawa ya aikata ya saba ma sashi na 145 na kundin hukunta manyan laifuka, don haka ya bukaci Kotu ta dage sauraron karar don bas hi damar gabatar mata da shaidunsa da zasu tabbatar da laifin Bawa.

Sai dai Bawa ya musanta aikata laifin, bayan haka sai lauyansa, Kayode Oyeyemi ya nemi Kotu ta bada belinsa, tare da bata tabbacin ba zai taba tserewa ba.

Jin hakan ya sanya Alkalin Kotun Adesoji Adegbye bada belin Bawa akan kudi Naira dubu hamsin da mutum guda da zai tsaya masa, shi ma zai biya kudi N50,000, daga nan ya dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel