Rundunar Yansanda ta fara binciken kwakwaf kan ayyukan matsafa a jihar Borno
Rundunar Yansandan jihar Borno ta sanar da fara gudanar da binciken kwakwaf game da rahoton da take samu daga jama’an sassan jihar daban daban game da ta’azzaran ayyukan matsafa a yankunansu, inji rahoton Premium Times.
Kwamishinan Yansandan jihar, Damian Chukwu ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaru, NAN, reshen jihar Borni a ranar Lahadi, 13 ga watan Mayu, inda yace sun ta’allaka bincikensu ne akan wasu munanan lamurra guda biyu dasuka faru a kwanakin baya.
KU KARANTA: BMusulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kwamishina Damian yana cewa sun bincike kan wani kisan gilla da aka yi ma wata budurwa, da kuma kwakule idanuwan wani mutumi mai shekaru 58 da karfi da yaji, dukkaninsu a garin Maiduguri.
Damina yace an tsinci gawar budurwar ne a wani dakin Otal, inda aka tarar da makogwaronta a yanke, yayin da aka kwakule idanuwan mutumin a unguwar rukunin gidajen 202, mutumin da ake ganin dan gudun hijira ne.
Bugu da kari kafin wadannnan lamurra su faru, sai da aka tsinci gawar wata karamar yarinya mai shekaru 7 da haihuwa a unguwar Mairi, inda mahaifinta mai suna Dogara Yohanna ya bayyana cewa sun kwashe kwanaki shidda suna nemanta tun bayan da mahaifiyarta ta aiketa siyo magi.
Sai dai wani mazaunin unguwar Tasham Bama, Ibrahim Wada ya bayyana cewa ba wannan ne farau ba, inda yace a baya ma sun samu faruwar irin wannan mummunan lamari sun kai guda 12, ya kara da cewa ya zama wajibi jami’an tsaro su shigo cikin lamarin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng