Ahir! Musulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada

Ahir! Musulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada

Musulman Duniya sun yi tarayya a nuna bacin ransu tare da sukar wata kamfani dake hada kayan maye da suka hada da giya da ire irensu dake kasar Jamus, wanda ta yi amfani da tutar kasar Saudiyya dake dauke da Kalmar Shada a hada kwalbar giyan.

Hotunan wannan giya ya watsu ne a shafukan yanar gizo da na sadarwar zamani, inda Musulmai suka bayyana wannan abu a matsayin cin fuskar addinin Musulunci, da Musulmai, da ma kasar Saudiyya gaba daya.

KU KARANTA: Son zuciya bacin zuciya: Yadda wasu matasa sun kashe kaninsu da duka akan rikicin wayar salula

Ahir! Musulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada
Kwalbar giyan

Musulmai da dama sun nemi kamafanin ta nemi afuwan Musulman Duniya, tare da janye giyan daga kasuwanni, musamman saboda Kalmar ‘La Ilaha Ilallah Muhammad Rasulullah’ dake rubuce baro baro a saman kwalbar giyan.

Sai dai a yayin da Musulmai ke tofin Allah tsine ga wannan kamfani, wata budurwa yar kasar Jamus Dora Gezwtscher ta bayyana cewa wai kamfanin ya buga kwalaban giya ne dake dauke da tutocin kasashe 32 da zasu fafata a gasar kwallon kafa ta Duniya da zai gudana a kasar Rasha, wannan ne dalilin da ya sanya su buga tutar kasar Saudiyya.

Ahir! Musulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada
Kwalbar

Legit.ng ta ruwaito ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake kasar Jamus ta yi Allah wadai da wannan cin fuska ga addinin Musulunci, kuma ta nesanta kanta da shi, inda tace ta tuntubi gwamnatin kasar Jamus, inda ta bayyana lamarin a matsayin wulakanta Kalmar shahada.

Daga karshe Ofishin Jakadancin Saudiyya ta bukaci gwamnatin kasar Jamus ta tilasta ma kamfanin neman afuwan kasar Saudiyya a rubuce da daukacin al’ummar Musulami, tare da tursasa ma kamfanin janye giyar daga kasuwanni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel