Yaki da yan bindiga: Yansandan Najeriya sun kama wani rikakken dan bindiga ‘Rambo’ a jihar Kaduna
Runduna ta musamman masu aiki da kwakwal na hukumar Yansandan Najeriya, IRT, ta samu nasarar cafke wani rikakken dan bindiga, da ya shahara a satar mutane, mai suna Ibrahim Barau, inkiya Rambo a jihar Kaduna, inji rahoton Legit.ng.
Rundunar Yansandan ta tabbatar da sunan dan bindigar ‘Rambo’, inda ta bayyana cewa ana kiransa da sunan ne saboda kwarewarsa a iya harbi, wanda har ta kai ga yana amfani da bindigu guda biyu, kirar AK 47 a lokaci guda.
KU KARANTA: Kisan jami’in ofishin jakadancin Najeriya: Jami’an tsaron kasar Sudar sun yi ram da makashinsa
Yansanda sun kara da cewe gungun Rambo ne ke addabar al’ummar karamar hukumar Birnin Gwari, hanyar Abuja-Kaduna-Kano da wasu yankuna na jihar Zamfara, kuma an kama shi ne yayin da yake tuka motarsa kirar Voksuwaja.
Legit.ng ta ruwaito an gano bindigu guda biyu, da alburusai guda hamsin da daya. Bugu da kari Yansandan sun kama wani dan bindigar mai suna Shehu Abdullahi Gashin Baki, mai shekaru 40, inda aka gano bindigu guda biyu, alburusai da dama.
Daga karshe Rundunar Yansandan ta bada tabbacin ba zata gajiya ba a kokarinta na ganin ta kakkabe jihar Kaduna daga matsalolin tsaro da take fuskanta, musamman na yin garkuwa da mutane da masu kashe mutane ba cas, ba as.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng