Dawowar Buhari: Atiku Abubakar yayi wa Shugaban kasa addu’a

Dawowar Buhari: Atiku Abubakar yayi wa Shugaban kasa addu’a

- Atiku Abubakar yayi magana bayan dawowar Shugaba Buhari gida

- Babban ‘Dan adawar dai ya roki Ubangiji ya karawa Shugaban lafiya

- Ana tunani Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fito takara a 2019

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar yayi magana bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga Ingila inda ya je domin Likitoci su kara duba lafiyar sa.

Dawowar Buhari: Atiku Abubakar yayi wa Shugaban kasa addu’a
Atiku Abubakar ya rokawa Shugaba Buhari karin lafiya

A shekaran jiya ne Wazirin Adamawa Atiku Abubakar yayi amfani da shafin sa sada zumunta na zamani na Tuwita ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murnar dawowa Najeriya. Shugaban kasar ya tafi Ingila ne domin ganin Likitocin sa.

KU KARANTA: Atiku ya bayyana yadda zai babbako da tattalin arziki idan ya samu mulki

Alhaji Atiku Abubakar wanda ya rike Mataimakin Shugaban kasa na shekaru 8 daga 1999 zuwa 2007 ya yayi wa Shugaba Muhammadu Buhari addu’a ya cigaba da samun koshin lafiya domin cigaba da aikin da Jama’an kasar su ka zabe shi.

A sakon da Atiku Abubakar ya isar a shafin na sa na Tuwita ya rokawa Shugaba Buhari karin lafiya da kuma kyawu a lamarun sa na sha’anin tafiyar da mulkin kasar. Shugaba Buhari dai ya dawo tun kafin ranar da ake tsammanin zai iso.

‘Dan takarar Shugaban kasar a zaben 2015 inda ya sha kasa hannun Muhammadu Buhari ya ajiye bambancin siyasa a gefe ya rokowa Shugaban kasar koshin lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel