Babban Sakataren Kungiyar CAN ya riga mu Gidan gaskiya

Babban Sakataren Kungiyar CAN ya riga mu Gidan gaskiya

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Dakta Musa Asake, Babban Sakataren kungiyar CAN (Christian Association of Nigeria) ya riga mu gidan gaskiya a wani asibiti bayan fama da wata 'yar gajeruwar lafiya da ta zamto sanadiyar ajalin sa.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, shugaban wannan kungiya Dakta Samson Olasupo Ayokunle shine ya bayar da sanarwa da sanadin Kakakin sa, Fasto Adebayo Oladeji.

Shugaban ya bayyana cewa ko shakka babu kungiyar ta yi babban rashi na Rabaran Osake wanda a kewarsa ta mamaye zukatan dukkanin abokan huldar sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, Marigayi Asake ya gamu da ajalin sa yana mai shekaru 66 a duniya.

Tarihi ya bayyana cewa, an haifi marigayi Asake a Unguwan Rimi ta gundumar Bajju-Kafanchan dake karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna a ranar 15 ga watan Satumba na 1952.

Marigayi Babban Sakataren Kungiyar CAN; Dakta Musa Asake
Marigayi Babban Sakataren Kungiyar CAN; Dakta Musa Asake

Nauyin wannan kungiya da marigayi Asake ya sauke na karshe shine ganawa da manema labari a ranar 27 ga watan Afrilu inda ya bayyana damuwar kan ci gaba da kashe-kashen da zubar a jinin al'umma a kasar nan.

KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta biya N439m ga mutane 14 da suka Busa Usir kan marasa biyan Haraji

A yayin haka ne Marigayi Asake ya kirayi daukacin mabiya addinin Kirista na kasar nan akan gudanra da zanga-zanga ta lumana da za ta yi tasriri akan gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro wajen zage dantsen na sauke nauyin da rataya a wuyan su.

Sakamakon wannan babban rashi na kungiyar CAN, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajinta tare da mika sakon ta'aziyyar sa ga kungiyar da sanadin kakakin sa, Mista Femi Adesina.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: