An soke zabukan kananan hukumomi biyu a jihar Kaduna

An soke zabukan kananan hukumomi biyu a jihar Kaduna

An soke zabuka a kananan hukumomi biyu cikin 23 da ke jihar Kaduna saboda matsalolin rashin ingantaccen tsaro sakamakon hari da wasu yan baranda suka kai ofishin hukumar zaben.

Ana halin yanzu mutane na jiran sakamakon zabukan da akayi a sauran kananan hukumomi 21 da ke jihar.

Ruwan sama da akayi kamar da bakin kwarya ya hana masu kada kuri'a fitowa sosai a wasu kananan hukumomi guda biyar da ke kudancin jihar.

An soke zabukkan kananan hukumomi biyu a jihar Kaduna
An soke zabukkan kananan hukumomi biyu a jihar Kaduna

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an tashi da ruwan sama ne kuma ruwan bai tsagaita ba har zuwa rana a kananan hukumomin da suka hada da Sanga, Zangon Kataf, Kaura da Jaba.

KU KARANTA: Bayan an yanke masa hukuncin daurin rai-dai-rai ya daba wa kansa kwalba a kotu

Rahotanni da muka samu sun bayyana cewa an samu tangarda a zaben kananan hukumomin Jaba da kaura yayin da wasu 'yan baranda suka yi awon gaba da kayayakin zaben.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce yan barandan sun kai hari ofishin hukumar zabe na jihar SIECOM, hakan yasa ma'aikatan hukumar suka ranta a na kare don su tsira da rayukansu.

A karamar hukumar Jaba, wasu masu kada kuri'an sunyi ta jira na tsawon lokaci idan suke tsamanin za'a cigaba da zaben duk da cewa ma'aikatan sun gudu.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce za'a saka sabon ranan da za'a sake zabukkan a kananan hukumomin da aka soke zabukkan.

Gwamnan ya ce hukumar zabe mai zaman kanta na jihar ta yanke shawarar cewa abinda yafi dacewa shine a dage zaben.

"Amma muna sa ran a yau za'a fidda sakamakon zabbukan kananan hukumomin guda 21.

"Kuma a halin yanzu muna gudanar da komi lami lafiya," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel