Malaysia ta zabi shugaban kasar da ya fi kowa tsufa a Duniya
A makon nan ne aka ga abin mamaki a siyasar Duniya inda Kasar Malaysia ta zabi Mahathir Mohammed a matsayin Firayim Minista wanda shi ne shugaban kasar ya fi kowa tsufa a Duniya. Mohathir ya buge wanda ke kan kujera a zaben da aka yi.
Mahathir Mohammed ya mulki Kasar Malaysia na fiye da shekaru 22 kafin ya sauka daga mulki a 2003. Nasarar da Jam’iyyar adawa ta samu karkashin Mahathir Mohammed yana nufin an ga karshen Jam’iyyar da ke mulki a kasar.
Jam’iyyar Barisan Nasional ta Kasar Malaysia wanda ita ce ke mulki fiye da shekaru 60 da su ka wuce ta sha kasa a zaben ban. BN ta samu kujeru kusan 80 ne kacal a Majalisar mutane 222 inda Jam’iyyar adawa ta lashe kujeru 113.
KU KARANTA: Ana yaki tsakanin tsohon Gwamnan PDP da EFCC a Kotu
Dr. Mohathir Mohammed ya ba Duniya mamaki da yayi nasara a wannan zabe inda ya zama shugaban kasar da ya fi kowa tsufa yanzu a Duniya. Dr. Mohathir ya girmi Shugaban kasar Amurka Trump har da ma Sarauniyar Ingila.
Nasarar da wannan tsohon ‘Dan siyasa ya samu ta girgiza Firayim Ministan da yake kan mulki watau Najib Razak. Yanzu haka dai har sabon shugaban kasar ya hana Najib Razak fita daga Malaysiya ya kuma tsige na-kusa da shi.
Ana dai zargin Shugaba Najib da satar dukiyar jama’a lokacin yana mulki don haka sabon Shugaban kasar ya nemi Jami’an kula da shiga-da-fice da su hana iyalin sa barin kasar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng