NSCDC sun kama wani tsohon dan sanda da wasu karti 18 da laifin latsa wata karamar yarinya

NSCDC sun kama wani tsohon dan sanda da wasu karti 18 da laifin latsa wata karamar yarinya

Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Jigawa ta ce jami'an ta sun kama wasu mutane 19 cikin har da tsohon dan sanda mai mukamin sufeta da ake zargi ta yin lalata da wata karamar yarinya yar shekaru 13.

Mai magana da yawun hukumar na jihar, SC Adamu Shehu ne ya tabbatar da kamun yayin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai (NAN) a yau asabar a garin Dutse.

NSCDC sun kama wani tsohon dan sanda da wasu karti 18 da laifin latsa wata karamar yarinya
NSCDC sun kama wani tsohon dan sanda da wasu karti 18 da laifin latsa wata karamar yarinya

Shehu ya ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar Alhamis misalin karfe 4 na yamma a garin Kiyawa da ke karamar hukumar Kiyawa da ke jihar na Jigawa. Ya ce hukumar ta kai cafke mutanen ne bayan surukin yarinyar ya shigar da kara a ofishin su.

KU KARANTA: An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

"Jami'an mu sun fara gudanar da bincike a kan lamarin kuma hakan ya kai ka kama wasu mutane 19 wadanda shekarun su ke tsakanin 25 - 60 cikinsu har da wani tsohon inspectan dan sanda mai murabus," inji Shehu.

Shehu ya cigaba da cewa, "Binciken da mukayi ya nuna cewa mutane da dama suna keta hakkin yarinayar wacce marainiya ne yayin da ta ke tallar Kunu, inda wasu daga cikinsu ke biyanta kudi kafin suyi lalata da ita wasu kuma suyi da mata alkawari kuma basu cikawa"

Mutane uku daga cikin wadanda aka kama sun amsa cewa sunyi lalata da yarinyar amma sauran sun musanta zargin da ake musu.

A cewarsa, wadanda suka amsa laifinsu sun gurafana gaban kuliya kuma tuni an aike da su gidan yari, sauran kuma za'a cigaba da bincike a kansu yayin da aka garzaya da yarinyar zuwa asibiti domin yi mata gwaje-gwaje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: