An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

- Dubun wani matashi ta cika bayan ya je sata a babban asibitin garin Kaduna

- Barawon dai ya yi shiga asibitin ne inda ya saje da masu jinyar marasa lafiya

- Daga bisani ya bari marasa lafiyan sunyi barci sai ya kwashe woyoyinsu amma bai san an kulle kofar fita ba

Wani barawo ya gamu da sakayyar Allah a yayin da ya shiga dakunan masu jinya da ke babban asibitin gwamnatin Kaduna na Yusuf Dan tsoho wanda akafi sani da asibitin dutse ya sace wa majinyata wayoyin salula.

An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa
An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

KU KARANTA: Bayan ya biya mata kudin karatu har digiri, ta sake shi saboda wai shi bai yi makaranta ba

Matashin dai ya shiga bangaren maza na asibitin ne inda ya saje da masu jinyar marasa lafiya sai dai ashe yana da wata maufa daban. Ya yi likimo a cikin dakin har zai da ya kura cewa barci ya kwashe marasa lafiyan sai ya zaga ya kwashe wayoyinsu.

An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa
An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

Sai dai bayan ya kama hanya zai fice sai ya tarar da cewa an kulle kofar dakin kamar yadda aka saba idan dare yayi saboda tsaro kamar yadda mujjalarmu ta ruwaito.

An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa
An damke shi bayan ya yi sata a asibiti amma kofa taki budewa

A dalilin hakan ne asirinsa ta tonu kuma bayan an kamashi, an mayar wa masu jinyar wayoyinsu sannan aka damka shi ga hannun jami'an tsaro da ke kula da asibitin inda zasu gudanar da bincike a kansa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164