Wata kungiyar Yarabawa ta kwance wa Obasanjo zani a kasuwa
Wata kungiyar yarabawa mai suna Yoruba Ronu Leadership Forum ta bayyana niyyar da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ke dashi wanda hakan ya sa ya ke da kokarin dakile taurariyar shugaban Muhammadu Buhari gabanin zaben 2019.
A wata sanarwa da sakataren kungiyar, Akin Malaolu ya fitar a daren jiya Juma'a, kungiyar ta ce Obasanjo kawai ya na kokarin damfarar yan Najeriya ne kamar yadda ya saba da habaicinsa da kuma kazafin da mutane sun gaji da saurara.
Wannan sanarwan ta fito ne bayan kwana daya da sanarwan da sabuwar jami'iyyar African Democratic Congress (ADC) da Obasanjo ya kafa ta sanar da cewa zata kori shugaba Buhari daga mulki a shekarar 2019.
KU KARANTA: Bayan ya biya mata kudin karatu har digiri, ta sake shi saboda wai shi bai yi makaranta ba
Kungiyar Yoruba Ronu, wanda suke goyon bayan mulkin shugaba Buhari, sun bayyana mamakinsu kan yadda wasu yan Najeriya ke sauraron irin makirce-makircen da tsohon shugaba Obasanjo ya ke kitsa wa.
"Ba za mu sa ida mu bari wasu shugabanin karya su rika aikata masha'a ba kawai don sun son su hambarar da gwamnnatin shugaba Muhammadu Buhari.
"Dole ne mambobin jam'iyyar APC su zage dantse saboda za'a fafata sosai a zabe mai zuwa, kuma za su yi nasara ne kawai ta hanyar tabbatar da adalci, gaskiya da walwala wanda sune halayen da suka sanya yan Najeriya goyon bayan gwamnatin shugaba Buhari har yanzu." inji kungiyar.
Kungiyar kuma ta ce duk wadanda basu son cigaba da tafiya da gwamnatin Buhari suna iya raba kama hanyarsu amma mafi yawancin yan Najeriya da kabilar yarabawa suna tare da shugaba Muhammadu Buhari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng