Yanzu-Yanzu: Garau na ke, inji shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ya kai ziyara kasar Amurka da kuma birnin Landan inda ya yi kwanaki hudu.
Jirgin shugaban kasar ta sauka a yammacin yau misalin karfe 6.45 a filin tashin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya tafi Landan don likitocinsa su sake duba lafiyarsa amma ya jadada wa yan Najeriya cewa lafiya lumui ya ke.
"Na tafi don likitocina su kara duba ni. Amma lafiya ta kalau," inji shugaban kasan.
KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya
Shugaban kasan ya baro Landan ne a ranar Talata kuma ana sa ran dawowarsa gida Najeriya gobe Asabar.
A halin yanzu dai ba'a bayyana dalilin da yasa shugaban kasan ya dawo a yau Juma'a ba maimakon Asabar da aka fadi a baya.
Wanda suka tarbi shugaban kasar sun hada da Ministan Abuja, Malam Musa Bello, Mataimakin Sufetan Yan sanda, Joshak Habila...
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng