Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya daga tafiyar da ya yi zuwa Landan don ganin likitansa.
Kamar yadda muka samo daga jaridar Daily Trust, jirgin shugaban kasar ya sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja misalin karfe 6.45 na yamma.
Wata sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a ranar Litinin ya ce, "A yayin da shugaban kasan ya tsaya don zuba mai a jirginsa a Landan a makon da ya wuce, shugaban kasan ya gana da likitocinsa."
KU KARANTA: An kama wasu 'yan sanda suna karban na goro a titi
Mr. Shehu ya ce likitocin shugaban kasan dama sun bukaci ya sake dawowa don su duba shi
Shugaban kasar ya tafi Landan din ne tun ranar Talata kuma wata majiyar ta ce ranar Asabar ne zai dawo.
A halin yanzu, ba'a san takamamen dalilin da ya sa shugaban kasan ya dawo kafin ranar Asabar din ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng