Bayan an yanke masa hukuncin daurin rai-dai-rai ya daba wa kansa kwalba a kotu

Bayan an yanke masa hukuncin daurin rai-dai-rai ya daba wa kansa kwalba a kotu

- Wani matashi mai suna Ajewole Dada yayi yunkurin kashe kansa bayan kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na har abada

- An sami matashin ne da laifin fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma fyade

- Bayan karanto masa hukuncin, Adewole ya rikice inda ya balle gilashin taga kuma ya daba wa kansa

A yau Juma'a ne wani matashi da aka zartas wa hukuncin zaman gidan yari na har abada, Ajewole Dada, ya tayar da hankalin kotu inda ya fasa gilashin tagar kotun kuma ya daba wa kansa ya kuma yi yunkurin raunana sauran mutanen da ke kotun.

Babban kotu jihar Ekiti ne ta zartas wa Ajewole da hukuncin bayan an same shi da laifukan da suka hada da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma yiwa wasu daliban kwalejin Ilimi na Ikere-Ekiti fyade a ranar 7 ga watan Nuwanban 2015 a hanyar Ikere-Igbara Odo.

Wani da aka yanke daurin rai-dai-rai ya daba wa kansa wuka a kotu
Wani da aka yanke daurin rai-dai-rai ya daba wa kansa wuka a kotu

DUBA WANNAN: Ga araha ga amfani: Fa'idoji 6 dake tattare da cin dabino

Yayin da alkalin kotun, Justice John Adeyeye ya karanto hukuncin, Ajewole ya dimauce, tare da fushi da rashin natsuwa bayan akawun kotun yayi masa yi masa bayanin abinda hukuncin ke nufi.

Alkalin ya ce masu shigar da karar sun gamsar da kotu tare da gabatar da hujojin da suka tabbatar da laifin wanda ake tuhuma.

Kotun ta rikice a yayin da ma'aikata da lauyoyi da sauran masu kallo suka firgita bisa abinda wanda ake yankewa hukuncin ya aikata sai dai jami'an tsaro sunyi gagawar rike shi saboda kada ya raunana wasu mutane a kotun.

Daga bisani, jami'an tsaron sun sanya masa ankwa kuma suka yi awon gaba dashi a cikin motar daukan masu laifi wato 'Black Maria'

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164