Gwamna El-Rufai ya bayyana dan siyasar da zai maye gurbin Shehu Sani a majalisar dattawa
Rikicin siyasar jihar Kaduna daya kunno kai a tsakanin gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Sanatocin jihar Kaduna, Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da kuma Sanata Danjuma Lar yayi kamari, inda ta kai ga gwamnan na barazanar kada su zabe.
Premium Times ta ruwaito El-Rufai ya bayyana wani hadiminsa, mashawarcinsa akan lamurran siyasa, Uba Sani a matsayin dan takarar da yake muradin ganin ya kada Sanata Shehu Sani a takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya a zabuka 2019.
KU KARANTA: Yansanda sun bindige mutane 2 a wani karanbatta da suka yi da jama’a a Legas
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin yakin neman zabe na shuwagabannin kananan hukumomi da yayi a mazabar sanatoriyar Kaduna ta tsakiya, inda ya yi kira ga jama’a da su tabbata sun kada Shehu Sani daga kujerarsa.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito El-Rufai ya mika kokon bararsa ga yayan jam’iyyar APC, da kuma jama’an gari dasu jajirce wajen ganin sun zabi Uba Sani a matsayin wakilin al’ummar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa.
Wannan kira da gwamnan yayi ya biyo bayan matakin tabbatar da takarar Uba Sani a matsayin sanata da shuwagabannin jam’iyyun APC na kananan hukumomi 6 cikin gida 7 da suka samar da Sanatoriya ta tsakiya suka yi ne.
Daga karshe gwamnan yayi kira ga jama’a da yan siyasa da kowa ya tabbata ya bi Doka da Oda a zaben kananan hukumomin jihar da zai gudana a ranar Asabar 12 ga watan Mayu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng