Ya kamata a fada mana cutar da ke damun Shugaban kasa - PDP

Ya kamata a fada mana cutar da ke damun Shugaban kasa - PDP

Mun samu labari cewa babban Jam’iyyar adawar Najeriya watau PDP ta fara hurowa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta ya fito ya fadawa Duniya ainihin cutar da ke damun sa.

Mutanen Najeriya sun fara kira Shugaban kasa ya bayyana rashin lafiyar sa
Mutanen Najeriya sun nemi a fada masu abin da ke damun Buhari

Jam’iyyar ta PDP tayi wannan kira ne bayan da Shugaban kasar ya kama hanya zuwa Landan domin ganin Likita. Wannan dai akalla shi ne karo na 4 da Shugaban kasar mai shekaru 75 ya tafi kasar asibiti a Kasar Birtaniya.

Kakakin Jam’iyyar PDP Kola Ologbodiyan yace akwai bukatar jama’a su ji takamammen abin da ke damun Shugaban kasar. yace ya kamata ayi wa ‘Yan kasa bayani mai gamsarwa domin da alamu abin ya wuce yadda ake tunani.

KU KARANTA: Wanda Shugaba Buhari ya ke goyon baya zai yi takara a APC

PDP ta zargi Shugaban kasa Buhari da labewa a Ingila kwanakin baya bayan ya gana da Shugaban kasar Amurka Donald Trump. Shugaban kasar dai yace ya tsaya yin wasu faci ne a Kasar Ingila amma ba wai Likita ya je gani ba.

Shi dai mai magana da yawun Shugaban kasar watau Garba Shehu yace babu shugaban kasar da ya taba bayyanawa Duniya larurar sa. Shehu yace Likitoci kurum za su duba Shugaban kasar kurum ne ba wai wani abu ba.

Dama jiya kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya na nema a rika ware kashi 1 cikin 100 na dukiyar Najeriya wajen harkar lafiya. Hakan zai inganta kananan asibitocin kasar da ake da su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng