Koci biyar da Arsenal ta ware domin maye gurbin Arsene Wenger

Koci biyar da Arsenal ta ware domin maye gurbin Arsene Wenger

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta datse jerin sunayen mutane da zasu maye gurbin Kocin kulob din da ya ajiye aikin sa, Arsene Wenger.

Kungiyar Arsenal tayi bankwana da Arsene Wenger a makon day a gabata amma dole ta dakata a kammala kakar wasannin kasashen Turai kafin samun Kociyan da zai maye gurbin Wenger.

An dade ana rade-radin Kociyoyi da kan iya maye gurbin Wenger, saidai yanzu kungiyar ta takaita neman ta tsakanin mutane biyar kacal.

1. Kocin Kungiyar Juventus, Max Allegri: Shine a sahun gaba a cikin mutanen da Arsenal ke burin maye gurbin Wenger das u saboda irin nasarar day a samu a shekaru 10 da suka wuce.

Koci biyar da Arsenal ta ware domin maye gurbin Arsene Wenger
Arsene Wenger

2. Patrick Viera: Tsohon dan wasar tsakia a kungiyar Arsenal kafin ya koma kungiyar Manchester City da taka leda, na daga cikin mutanen da kungiyar Arsenal ke tunanin maye gurbin Wenger da su.

3. Mikel Arteta: Shi ma tsohon dan was an kungiyar Arsenal ne dake da goyon bayan wasu jiga-jigai a masu ruwa da tsaki a harkokin tafiyar da kungiyar Arsenal.

DUBA WANNAN: Matan Gwamnonin Arewa sun dauki kudirin kawar da wata babbar matsala a yankin

4. Julian Nagelsman: Kocin kungiyar Hoffenheim ta kasar Jamus. Matashi ne, kamar Arteta, da kungiyar ke nazari a kan sa da kuma tuananin ko zai iya maye gurbin Wenger.

5. Kocin kungiyar Monaco, Leonardo Jardim: Ya taka rawar gani a jagorancin kungiyar Monaco dake kasar France. Kungiyar Arsenal ta saka sunan sa cikin kocin da take burin zai iya maye gurbin wenger.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel