Hukuma sai rarrashi: Gwamnatin jihar Katsina ta garkame ofishin kamfanin sadarwa na Glo

Hukuma sai rarrashi: Gwamnatin jihar Katsina ta garkame ofishin kamfanin sadarwa na Glo

Da safiyar yau, Alhamis, ne gwamnatin jihar Katsina ta garkame ofishin kamfanin sadarwa na Glo saboda tirjewar kamfanin na kin biyan kudaden haraji na tsawon shekaru hudu.

Gwamnatin ta rufe ofisoshin kamfanin dake barikin ‘yan sanda da kuma ofishin karba da kulawa da korafin abokan cinikin kamfanin dake Kofar Kaura, duk a garin Katsina.

Hukuma sai rarrashi: Gwamnatin jihar Katsina ta garkame ofishin kamfanin sadarwa na Glo
Kamfanin sadarwa na Glo

Nadada ya bayyana cewar suna bin kamfanin kudin haraji na tsawon shekaru hudu da yawan su ya kai miliyan N400, kuma har shelkwatar kamfanin dake Legas suka kaiwa takardar neman su biya harajin amma suka yi burus da batun.

Shugaban hukumar raya karkara da birane a jihar, Usman Nadada, ya jagoranci jami’an gwamnatin jihar da jami’an tsaro aka rufe ofisoshin saboda kunnen uwar shegu da kamfanin ya yi masu bayan sun nemi ya biya kudin harajin.

DUBA WANNAN: Ya kwakule zuciya da idon mahaifiyar sa bayan ya kashe ta saboda ya yi kudi

Nadada ya kara da cewa duk ragowar kamfanonin sadarwa na biyan harajin su a kan lokaci amma kamfanin Glo ya gaza biyan harajin duk da kasancewar sau shida gwamnatin jihar na aike masu da takardar tuni. Hakan ya saka gwamnatin bata da wani zabi day a rage face ta rufe ofisoshin kamfanin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel