'Yan Najeriya sun kosa a kammala babbar hanyar Legas - Lai Muhammed
- Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed yace' yan Najeriya sun kosa suga an kammala babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan don su fara amfana da ita
- Ministan ya fadi hakan ne a wani duba aikin da sukayi na tsawon kilometers 127 wanda kamfanin Julius Berger Nigeria Plc da Reynolds construction company (RCC) sukayi
Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed yace' yan Najeriya sun kosa suga an kammala babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan don su fara amfana da ita.
Ministan ya fadi hakan ne a wani duba aikin da sukayi na tsawon kilometers 127 wanda kamfanin Julius Berger Nigeria Plc da Reynolds construction company (RCC) sukayi.
DUBA WANNAN: Tsoho dan shekara 92 ya zama shugaban kasa
A maganar da yayi a garin Shagamu na jihar Ogun a ranar Larabar nan, Ministan yace aikin da aka kammala a yanzu, hankalin masu amfani da titin ya fara kwanciya.
Yace, tashin hankali hatsarurruka, fashi da makami, garkuwa da mutane, kwace da kuma bacin lokaci da ake samu a titin an magance shi.
"Munyi tafiya a titin daga Legas zuwa Ibadan kuma munyi farinciki da ganin gyaran da aka samu."
"Babu tantama cewa, a aikin da aka kammala zai rage bata lokaci wurin tafiye-tafiye a titin. A da, mutane har kwana suke a hanyar nan, amma yanzu zaka iya zuwa Ibadan cikin awa daya da rabi. Gaskiya wannan abin jinjiinawa ne."
"An rage yawan hatsarurruka sosai, a yanzu mutane zasu iya tafiya hankalinsu kwance da kuma tabbacin tsaro. Fashi da makami da kuma garkuwa da mutane yayi sauki a cusasshen titi. Amma yanzu da titin yake a gyare, an rage rabin wadannan matsalolin."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng