Murna baki har kunne: Kano ta samu sabuwar Jami’a mai zaman kanta ta farko

Murna baki har kunne: Kano ta samu sabuwar Jami’a mai zaman kanta ta farko

- Jihar Kano na cigaba da yiwa tsaranta nisa a yawan Jami'o'i a Arewacin Najeriya

- Wannan zuwa bayan sake amincewa da kafa wata Jami'a irinta ta farko a Kano, kuma wata na kan hanya

Karamin Minista a ma’aikatar Ilimi ta kasa Anthony Anwuka, ya tabbatar da amicewar majalisar zartarwa na samar da sabuwar jami’a mai zaman kanta mai suna Skyline University.

Murna baki har kunne: Kano ta samu Jami’a mai zaman kanta ta farko
Murna baki har kunne: Kano ta samu Jami’a mai zaman kanta ta farko

KU KARANTA: Babu kaskantattu kamar masu yunkurin kawo sauyi a Kur'ani - Shugaban kasar Turkiyya

Duk da yawan jami’o’in da jihar Kano take da su na Gwamnatin tarayya biyu wato Jami'ar Bayero ta Kano da Jami'ar karatun aikin 'Dan sanda dake Wudi, da na jihar biyu Jami'ar kimiyya da fasaha ta Wudil da Jami'ar Maitama Sule wato tsohuwar Northwest Univerity, sai kuma wannan ta farko mai zaman kanta da hukuma ta amince da ita.

Jihar Kano ita ce jiha mafiyawan Mutane a duk fadin kasar nan wanda hakan ya sanya take da kaso mai yawa na daliban da suke neman guraben karatu don zurfafa karatun a manyan makarantu amma sai dai kash yunkurin nasu na gaza kaiwa ga gaci sakamakon karancin guraben karatu da makarantun jihar ke bayarwa.

Kafuwar wannan Jami'a dai zai saukaka cunkosan neman Jami'o'in Gwamnati kacal da ake da su a jihar.

Yanzu haka akwai wata jami’ar dake jiran sahalewar hukuma ita ma mai zaman kanta da akaiwa lakabi da Attanzil University.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel