Atiku zai gina wata katafaren asibitin kudi a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yana daya daga cikin manyan masu saka jari a Najeriya
- Atiku yana da masana'antu da dama a sassa daban-daban na Najeriya kuma duk ana damawa da su
- A yanzu, tsohon shugaban kasan ya fara mayar da hankali fannin samar da lafiya
Wata kamfani mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar mai suna Africa Health za ta gina wani sabin asibiti mai gadaje 100 a babban birnin tarayya Abuja.
Turakin Adamawan dai yana daya daga cikin manya-manyan masu saka jarri a Najeriya kuma yana da kamfanoni da masana'antu masu yawa a sassa daban-daban na Najeriya wanda ake gogaya da su a fanin su.
Tsohon shugaban kasan ya fada harkar kasuwanci ne tsundum tun bayan da ya yi murabus daga aikin Kwastam a watan Afrilun shekarar 1989.
"Ina farin cikin ganawa da tawagar mahukuntan wata asibiti malakar yan kasar Saudiyya da Jamus karkashin jagorancin Dr. Rajeev Kaushal inda muka tattauna hadin gwiwa da zamuyi da kamfanina Africaan Health Services wajen kafa wata asibiti mai gadaje 100 a Abuja," Kamar yadda Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter.
Atiku ya yi wannan sanarwan ne kwana daya bayan ya bayar da gudunmawar naira miliyan 10 don kulawa da mutanen da fashewar bam a garin Adamawa ya yi wa rauni.
Tsohon mataimakin shugaban kasan dai an san shi da kyauta sosai, hakan yasa magoya bayansa suke tare dashi cikin rintsi da walwala tsawon shekaru masu yawa.
Ana sa ran Atiku zaiyi takaran zaben fidda gwami a jam'iyyar PDP gabanin zaben shugabancin kasa a shekarar 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng