Magoya bayan Atiku zasu hada gagarumin taro a Abuja

Magoya bayan Atiku zasu hada gagarumin taro a Abuja

- Wasu matasa magoya bayan Atiku Abubakar zasu kaddamar da wani gagarumin taro a Abuja

- Taron wanda zai tattaro matasa kimanin Miliyan Biyar, domin nuna goyon bayan su ga tsohon shugaban kasar

- Akwai yiyuwar jam'iyyar PDP ta tsayar da Atiku a matsayin dan takarar ta na shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019

Magoya bayan Atiku zasu hada gagarumin taro a Abuja
Magoya bayan Atiku zasu hada gagarumin taro a Abuja

Wata kungiya ta matasa magoya bayan Atiku Abubakar, tace zata shirya wani gagarumin taro na kimanin matasa miliyan biyar, domin yawon kamfen da kuma nuna goyon bayan su ga tsohon mataimakin shugaban kasar akan niyyar shi ta fitowa takarar shugaban kasa, za ayi taron ne a cikin birnin Abuja.

DUBA WANNAN: El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan korar 'yan NYSC

Shugaban masu gudanar da taron, Adegboyega Adeleke, wanda ya bayyana hakan yayin da aka kaddamar da wata kungiya mai suna '#Unstoppable Atiku 2019' a jihar Kaduna, shugaban yace matasan Najeriya basa jin dadin irin mulkin da wannan gwamnatin take gabatarwa.

Yace a irin wannan yanayi da kasar nan take ciki na matsalar tattalin arziki, dolene Najeriya ta bukaci jajircaccen shugaba wanda zai kawo cigaba ga kasa da al'ummar kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng