An jefe wata mata har lahira saboda auren maza
An jefe matar ne saboda ta auri namiji fiye da daya, kamar yadda wani shafi mai alaka da kungiyar ya sanar.
Matar, Shukri Abdullahi Warsame, ta auri maza 11 ba tare da mutuwar aure tsakanin ta da namji koda daya daga cikin su ba.
Mayakan kungiyar al-shabab sun tona rami har wuya inda suka saka matar suka binne kafin su jefe ta har lahira a garin Sabale dake yankin Lower Shabelle.
Shafin ya bayyana cewar matar na cikin koshin lafiya kafin a jefe ta, sannan kuma ta amsa laifin ta.
Ko a shekarar 2014 saida kungiyar al-shabab ta jefe wata mata saboda auren maza hudu a boye a kudancin lardin Barawe.
DUBA WANNAN: Hotunan sabon ginin shelkwatar hukumar EFCC da aka gina a kan biliyan N24
Mayakan al-shabab na cigaba da rasa ikon yankunan da take rike da su ga gwamnatin kasar Somalia mai goyon bayan Tarayyar Afrika.
A inda suke da iko, kungiyar al-shabab na cigaba da cin karen ta babu babbaka.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng