Gwamnatin tarayya ta fadawa jami’o’in tarayya cewa kudin makaranta ya sabawa doka

Gwamnatin tarayya ta fadawa jami’o’in tarayya cewa kudin makaranta ya sabawa doka

- Kungiyar tarayya a ranar Laraba cewa babu wata jami’ar tarayya da ya kamata ta karbi kudi daga hannun dalibai saboda doka bata amince da hakan ba

- Ministan ilimi na jiha Anthony Anwuka, ya bayyana haka bayan ganawarsu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

- Ministan yace kungiyar ta tattauna game da kudaden da ake karba daga hannun dalibai, inda yace a dokar kasa babu jami’ar tarayya da ya kamata ta karbi kudi daga hannun dalibai

Kungiyar tarayya a ranar Laraba cewa babu wata jami’ar tarayya da ya kamata ta karbi kudi daga hannun dalibai saboda doka bata amince da hakan ba.

Ministan ilimi na jiha Anthony Anwuka, ya bayyanawa manemin labarai na gidan gwamnati haka bayan ganawarsu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Gwamnatin tarayya ta fadawa jami’o’in tarayya cewa kudin makaranta ya sabawa doka
Gwamnatin tarayya ta fadawa jami’o’in tarayya cewa kudin makaranta ya sabawa doka

Ministan yace kungiyar ta tattauna game da kudaden da ake karba daga hannun dalibai, inda yace “a dokar kasa babu jami’ar tarayya da ya kamata ta karbi kudi daga hannun dalibai.”

KU KARANTA KUA: Dangote ya sake shiga jerin fitattun mutane 75 a duniya

Anwuka yace kungiyar ta fahimci cewa wasu jami’o’in suna karbar kudi dagane da yawan darussan da daliban keyi, inda yace gwamnatin zatayi bincike akan lamarin don ta hana yin hakan sannan kuma an bawa kungiyar jami’o’in umurnin bincike akan lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng