Tayar jirgin Air Peace ta fashe yayin sauka a jihar Legas

Tayar jirgin Air Peace ta fashe yayin sauka a jihar Legas

A ranar Talata, 23 ga watan Yulin 2019, mun samu cewa daya daga cikin tayoyin wani jirgin Air Peace ta fashe yayin dirarsa a filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammad International Airport MMIA dake jihar Legas.

Duk da babu ko kwarzane na jin rauni ballatana salwantar rayuka, sai dai an auna tsautsayi yayin da tayar jirgin sama na kamfanin Air Peace ta fashe wanda ya taso daga birnin Fatakwal na jihar Ribas kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito.

Hoton jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Hoton jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Asali: Facebook

Hoton jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Hoton jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Asali: Facebook

Wani sashe na jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Wani sashe na jirgin Air Peace da tayarsa ta fashe a jihar Legas
Asali: Facebook

Daya daga cikin fasinjoji yayin labartawa manema labarai bahasin wannan mummunan tsautsayi, ya ce jirgin bayan dirar sa cikin gaggawa ya kuma kauce daga kan hanyarsa inda yayi tafiya ta wani takaitaccen zango a shagide.

Cibiyar bincike a kan aukuwar hadurra, AIB, Accident Investigation Bureau, ta fara gudanar da bincike domin gano makasudin aukuwar wannan tsautsayi.

Kakakin hukumar kula da tashoshin jiragen sama na Najeriya, Henrietta Yakubu, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan lamari da ko shakka babu a cewar sa an auna tsautsayi.

KARANTA KUMA: Dalilin ci gaba da kashe-kashe a jihar Zamfara duk da haramcin hako ma'adanai - Hukumar Soji

A na iya tuna cewa, makamancin wannan tsautsayi da ya auku a filin jirgin saman garin Abuja ya jefa fasinjoji cikin razani yayin da tayar jirgin saman na kamfanin Air Peace ta fashe a watan Janairun da ya gabata.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: