Yanzu-Yanzu: Majalisar Wakilai ta umurci 'yan sanda su bude hedkwatan Peace Corps
Bayan nazarin rahoton da kwamitin sauraron korafin jama'a na Majalisa ya gabatar, Majalisar ta cinma matsaya inda ta umurci hukumar yan sandan Najeriya ta bude hedkwatan ofishin Peace Corps da ke Abuja.
Majalisar ta bawa hukumar yan sandan kwanaki 21 su kwashe motocin da suka girke a gaban ofishin kuma su bude.
Kwamitin majalisar da gudanar da bincikem ne bayan wasu kungiyoyin sa kai sun shigar da kara inda suka roki Majalisar ta shiga tsakani cikin rikicin saboda a ceto demokradiyar Najeriya.
KU KARANTA: Wani hazikin dan Najeriya ya kera mota mai lafiya da N80,000 kacal
A ranar 9 ga watan Nuwamban 2017, wata babban kotun tarayya ta umurci hukumar yan ta sanda su bude hedkwatan na Peace Corps tare da biyansu diyyar naira miliyan 12.5.
Kazalika, wata kotun tarayyar da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar 15 ga watan Janairun 2018 ta umurci hukumar na yan sanda su kwashe yanasu-yanasu su bar harabar hukumar ta Peace Corps.
A yayin da yake gabatar da rohoton kwamitin a gaban majalisa yau Laraba, Ciyaman din kwamitin sauraron karan mutane, Nkem Abonta ya ce wannan ba shine karo na farko da Babban Sufetan yan sandan ya ke kin amsa gayyatar da majalisar keyi masa ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng