Shugabannin Najeriya sun jajintawa Rasuwar Sheikh Isyaka Rabi'u
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje cikin damuwar rashi da jimami ya jajinta tare da mika ta'aziyyar sa dangane da rasuwar gawurttaccen dan Kasuwa kuma babban malami, Shiekh Khalifa Isyaka Rabi'u.
Marigayi Khalifa Isyaku Rabi'u wanda shine jagoran mabiya darikar Tijjaniya na nahiyyar Afirka ya riga mu gidan gaskiya ne a ranar Talatar da ta gabata a bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya inda ya cika a wani asibitin birnin Landan na kasar Birtaniya.
Cikin wata sanarwa da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba, gwamna Ganduje ya mika ta'aziyyar sa ga iyalan marigayi Khalifa da kuma daukacin musulmai na Najeriya da duniya baki daya.
Hakazalika shugaban majalisar wakilai, Honarabul Yakubu Dogara ya mika na sa sakon ta'aziyyar ga iyalan Marigayi Sheikh Khalifa da ya rasu yana mai shekaru 90 a duniya.
KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya ta malalo N3trn domin ci gaban gine-gine a Najeriya
A cikin sanarwar ta jajintawa da ta'aziyya, Honarabul ya Dogara ya bayyana cewa hakika wannan babban rashi ne ga Kanawa watau al'ummar jihar Kano da kuma ilahirin mabiya darikar Tijjaniya na duniya baki daya.
Dogara ya kuma roki Ubangijin Talikai akan ya gafarci kurakuran marigayi Khadimul Islama wanda ya kasance wani jigo cikin jihar Kano da kuma shahara akan sadaukar da dukiyar sa wajen kyautatawa talakawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng