Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari ga iyalan Shehu Isyaku Rabi'u da Kanawa

Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari ga iyalan Shehu Isyaku Rabi'u da Kanawa

- Shugaba Buhari ya rubuto kasida ta rashin babban malami da aka yi a Kano

- Ya taba kama dattijon a mulkinsa na soja a 1985

- Isiyaka Rabiu dattijon kirki ne da ya rayu a Kano

Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari ga iyalan Shehu Isyaku Rabi'u da Kanawa
Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari ga iyalan Shehu Isyaku Rabi'u da Kanawa

Shugaba Muhammadu Buhari, ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, ya aiko ta'aziyyarsa ga maluman Kano, da ma jama'arta, kan rasuwar Alhaji Isyaka Rabiu, hamshakin dan-kasuwa da ya rasu a daren jiya.

A sanarwar, shugaban yayi alhinin rashin babban malamin, inda ya kira shi da dattijon arziki, dan kasuwa da malami, wanda kowa zaiyi rashi, a fadin kasar nan.

DUBA WANNAN: Kannywood: Moda yace bai mutu ba

'Rashin na Malam, wani babban rashi ne ga Malumta, karatu, da ma kasuwanci, wanda kowa ke jimami. Dattijon, ya bar baya mai kyau, muna fatan iyalansa zasu dora kan ayyukansa na alheri, musamman kasuwanci da samarwa samari ayyukan yi, muna fata Allah ya rahamshe shi, ya yafe masa zunubbansa, ya kuma kyautata bayansa.'

A shekarun mulkin soja dai, shugaba Buhari ya daure Malamin bisa zargin almundahana da boye abinci don yayi tsada, amma an sako shi ba tare da samun laifinsa a kotu ba. Sai dai an zargi sojoji da cuzgunawa da ma fasa rumbunan ajiyar abincin 'yan kasuwar lokacin, inda aka raba wa talakawa.

Rade-radi da suka yi ta yawo kan dattijon da cewa wai yana yanka kai, kuma wai matsafi ne wanda wai ya saci marigayi wazirin Kano, Sheikh Isa Waziri, duk sun zamo sharri ne kawai ake wa malamin saboda jahiltar kirkinsa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel