Dalibai sun ragargaji malaman su saboda sun hana su satar amsa yayin jarrabawar WAEC
Daliban aji na karshe na makarantar sakandire na Zabzugu Senior High School da ke yankin Zabzugu na kasar Ghana sun dauki miyagun makamai da duwatsu kuma suka kaiwa malaman makarantar farmaki saboda sun ki barin su suyi satar amsa a jarabawar WAEC.
Kamar yadda Adomonline ya ruwaito, fusatattun daliban sun baranat kayayakin makaranta da dama wanda suka hada da kofofi, tagogi, talabijin da sauransu. Daliban sunyi ikirarin cewa an tauye musu hakkin su na shiga dakin jarabawa da takardunsu don suyi satar amsa.
Wani dalibi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, duk da cewa ba su yi wata yarjejeniya da malaman makarantan na barin su suyi satar amsa ba, suna da masaniya cewa malaman wasu makarantun suna barin daliban su suyi satar amsar.
KU KARANTA: Wani hazikin dan Najeriya ya kera mota mai lafiya da N80,000 kacal
Wani malamin makarantar da ya tabbatar da afkuwar lamarin yace laifin su kawai shine kin amincewa daliban suyi satar amsa a jarabawar na WAEC. Ya kara da cewa ya tsira da ransa ne saboda bai tsaya a gidansa ba domin daliban su tafi gidansa da duwatsu sunyi kacha-kacha da gidan.
Ya ce, "Daliban suna ikirarin cewa suna da damar shiga dakin jarabawa da litafan karatunsu don suyi satar amsa amma ni ban san wata dokar jarabawa da ta amince da hakan ba. Saboda kin amincewar da mukayi, daliban su shiga makaranta dauke da makamai inda suka rika barna kuma sukayi ikirarin kashe duk wanda suka samu."
Malaman makarantan sun dauki alwashin ba zasu sake komawa makarantar ba har sai gwamnati ta samar da ingantaccen tsaro.
Shugaban yankin na Zabzugu, Honarabul Iddi Ahmed ya yi kira ga hukumomin tsaro su tabbatar cewa sun warware rikicin da ke faruwa tsakanin daliban da malaman su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng