Mutuwar Isiyaka Rabiu: Mu mahaddata mun yi rashi, Attajirai ma sun yi rashi – Dahiru Bauchi

Mutuwar Isiyaka Rabiu: Mu mahaddata mun yi rashi, Attajirai ma sun yi rashi – Dahiru Bauchi

Fitaccen Malamin darika, Malam Dahiru Bauchi ya jajanta ma iyalan marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu tare da al’umma, masarauta da gwamnatin jihar Kano, inda yace an tafka babban rashi, inji rahoton Rariya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dahiru Bauchi yana cewa Allah ya yi ma Rabiu wata muhimmin baiwa a tsakanin daliban Shehi Ibrahim Nyass, wanda shi kadai ke da ita, ba shi da na biyunsa.

KU KARANTA: Mutane 3 Uku sun mutu a wani tashin tashin da ya wakana a jihar Nassarawa

“Ka bada darussan karatun Qur’ani, sa’annan ka tafi ka bude Kanti a kasuwa, ku kuma dawowa gida ka bude wafifa a zawiyyarka, sa’annan ka hidimtawa yayan Shehu Ibrahim Nyass, sai Isiyaka Rabiu.” Inji Shehi.

Mutuwar Isiyaka Rabiu: Mu mahaddata mun yi rashi, Attajirai ma sun yi rashi – Dahiru Bauchi
Isiyaka Rabiu da Dahiru Bauchi

Shehi Dahiru Bauchi ya bayyana cewa: “Mu mahaddata mun yi rashin dan uwanmu mahaddaci, mun yan Tijjaniyya mun yi rashin dan uwanmu dan Tijjaniyya, haka zalika masu kudi sun yi rashin dan uwansu mai kudi.”

Daga karshe Shehin Malamin ya karkare jawabinsa da cewa: “Ina yi ma gwamnatin jihar Kano, da masarautar Kano ta’aziyya wannan babban rashi da aka yi, Allah ya gafarta masa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng