Yanzu Yanzu: Yan kunar bakin wake mata 2 sun tayar da kansu Maiduguri
A ranar Laraba, 9 ga watan Mayu, kakakinn hukumar bayar da agajin gaggawa na shiyar Arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim ya tabbatar da cewa wasu yan kunar bakin wake mata biyu sun tayar da kansu a kusa da wani masallaci a Maiduguri, babban birnin jihar Boirno.
Ibrahim yace yan kunar bakin waken sunyi yunkurin shiga wani masallaci a yankin Jiddari dake Maiduguri yayinda masallata ke sallar subhi a ranar Laraba, amma mazauna wajen dake lura suka kora su. Daily Sun ta ruwaito.
An samu labarin cewa bama-baman sun tashi a jikinsu yayinda suka fadi a makarantar Firamare na Jiddari yayinda sukayi kokarin guduwa daga yankin, inji mazauna wajen.
Lamarin ya faru ne da misalign karfe 5:08 na safiyar Laraba, cewar kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa na shiyar Arewa maso gabas, Abdulkadir Ibrahim.
KU KARANTA KUMA: Masu kula da shugaba Buhari na boye rashin lafiyarsa – PDP
Sannan kuma an tattaro cewa babu wanda ya rasa ransa baya ga yan kunar bakin waken.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng