Ina ma Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP – Inji tsohon gwamnan Kano Shekarau

Ina ma Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP – Inji tsohon gwamnan Kano Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa ba karamar farin ciki zai yi ba da ace magajinsa, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso zai dawo cikin tafiyarsu a jam’iyyar PDP, inji rahoton BBC Hausa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shekarau ya bayyana haka ne a cikin wata hira da yayi da ita, inda yace a tun bayan da ya mika ma Kwankwaso mulki a shekarar 2011, basu taba magana ba, ko a waya, kuma sai daya suka hadu da juna, shi ma a cikin jirgin sama.

KU KARANTA: Abin kunya: Yadda wani Uba da Dansa suka zakke ma wata Yarinya mai shekaru 9 a Katsina

Zuwa yanzu dai maganganu sun yi yawaita na cewa wai tsohon gwamna Kwankwaso zai sauya sheka zuwa PDP sakamakon rikicin gida da ya dabaiba dangatakarsa da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Ina ma Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP – Inji tsohon gwamnan Kano Shekarau
Shekarau

Sai dai game da rade radin da ake yin a cewa shigar Kwankwaso APC ce ta yi sanadin fitar Malam Shekarai daga jam’iyyar zuwa PDP, Malam yace ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana, duk da yake dai sanannen abu ne cewa jigogin biyu basa ga maciji a siyasance.

Wani lura a nan shi ne daga kwankwaso har Shekarau, dukkaninsu manyan yan siyasa ne, kuma sun mulki jihar Kano tsawon shekaru takwas takwas, haka zalika suna da dimbin magoya baya, bugu da kari dukkaninsu sun tsaya takarar shugaban kasa a baya.

Ina ma Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP – Inji tsohon gwamnan Kano Shekarau
Hannun karba, hannun mayarwa

Duba da wadannan alkalumma ne ake ganin idan da zasu hada kai, su zauna cikin jam’iyya guda, da lallai zasu zamo ma jam’iyyar APC tarnaki a zaben 2019, musamman a jihar Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng