Abin kunya: Yadda wani Uba da Dansa suka zakke ma wata Yarinya mai shekaru 9 a Katsina

Abin kunya: Yadda wani Uba da Dansa suka zakke ma wata Yarinya mai shekaru 9 a Katsina

Wani Magidanci mai shekaru 60, Lawal Angala tare da dansa, Isah Lawal mai shekaru 19 sun gamu da fushin Kotu bayan ta kamasu da laifin yi ma wata karamar yarinya mai shekaru 9 fyade a jihar Katsina, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Alkalin Kotun, Fadila Dikko ce ta umarci a daure mata Uba da dan, a Kurkuku har zuwa ranar 14 ga watan Yuni don cigaba da sauraron karar da aka shigar dasu a gabanta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Turnuku: An kwashi yan kallo a wani hari da Sojoji suka kai ma Yansanda a Legas

Dansanda mai shigar da kara, ya bayyana ma Kotu cewa wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar 2 ga watan Mayu a kauyen Safana na jihar Katsina, kamar yadda mahaifiyar yarinyar, Shamsiyya Abdullahi ta shaida ma Yansanda a yayin da ta kai kararsa.

Dansandan ya cigaba da shaida ma Kotun cewar Uban da dan sun tura yarinyar zuwa dakinsu, inda suka yi mata layi suna yi mata fyade, ya kara da cewa laifin ya saba ma sashi na 283 na kundin tsari mulki.

Sai dai wadanda ake tuhumar sun nemi Kotu ta yi musu sauki, amma Alkali Fadila Dikko ta yi watsi da bukatarsu, inda tace babu wanda ke da hurumin sauraron karar tasu idan ba babbar Kotu ba, daga nan sai Dansandan yace suna cigaba da gudanar da bincike, don haka ya bukaci a basu sabon ranar sauraron kara.

A wani labarin kuma, wani matashi mai shekaru 20, Hassan Sule ya gamu da hukuncin dauri bayan Kotu ta kama shi da laifin yi ma wata mata mai shekaru 50, Salamatu Adamu tare da yin barazanar kashe taa kauyen Dantakum dake cikin karamar hukumar Dan Musa na jihar Katsina.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng