Mai martaba Sarkin Katsina ya nada sabon Babban Limamin jihar Katsina (Hoto)

Mai martaba Sarkin Katsina ya nada sabon Babban Limamin jihar Katsina (Hoto)

Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman ya nada Malam Gambo Mustapha Amdu Ratibi a matsayin sabon babban Limamin masarautar Katsina, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kafin nadinsa, Malam Amadu, shi ne mataimakin marigayi tsohon babban Limamin jihar Katsina, wanda ya rasu a ranar Lahadin data gabat yana da shekaru 95 a rayuwa.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Sojoji sun cika hannayensu da wasu yan bindiga guda 6 a jihar Benuwe

Sakataren masarauta, sallaman Katsina, Bello Ifo ne ya tabbatar da nadin Malam Amadu, inda yace mai marataba Sarkin Katsina ya nada Malam Dayyabu a matsayin Ratibin Liman.

Mai martaba Sarkin Katsina ya nada sabon Babban Limamin jihar Katsina (Hoto)
Gambo Amadu

Sallaman na masarautar jihar Katsina, ya bayyana cewa za’a nada Limaman biyu ne da sabon mukamansu a ranar Juma’a 10 ga 11 ga watan Mayu a fadar Sarkin Katsina, bayan nan ana sa ran sabon babban Limamin zai jagoranci Sallar Juma’a a babban Masallacin jihar.

A wani labarin kuma, shahararren Malamin adiinin Musluncin nan na jihar Kano, Sheikh Isiyaka Rabiu ya rasu a ranar Talata 8 ga watan Mayu a birnin Landan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel