An sake kwatawa: Sojoji sun cika hannayensu da wasu yan bindiga guda 6 a jihar Benuwe
Rundunar Sojin kasa ta Najeriya ta samu nasarar damke wasu yan bindiga da suka fito daga kabilar Tibi har guda shidda dauke da muggan makamai a kauyen Tse-Dum, dake mazabar Mbawa a cikin karamar hukumar Guma na jihar Benuwe.
Daily Trust ta ruwaito Kwamdandan runduna ta 72 na Dakarun Sojin kasa, Suleiman Muhamamd ne ya sanar da haka a yayin da yake gabatar da yan bindigan ga manema labaru, inda yace Sojoji na musamman na Birget ta 707 ne suka kama yan bindigan yayin wata samame.
KU KARANTA: Allah ya yi ma Dan uwan shahararren dan wasan Najeriya Rashidi Yakini rasuwa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikin yan bindigan ya sheka barzahu a sanadiyyar musayar wuta da suka yi da Dakarun Soji, sa’anna ya bayyana sunayen sauran yan bindigan guda biyar kamar haka; John Yobeh, Terso Nyaku, Agboh Ukume, Thomas Adum da Faaga Uereyev.
Sai dai a tattaunawa da guda cikin yan bindigar, Ukume yayi da manema labaru, ya bayyana cewa wasu yan Fulani yan bindiga ne suka afka ma kauyensu, inda suka sace daya daga cikin abokansu, ya kara da cewa sun gano sansanin yan Fulanin, kuma sun dauko gawar dan uwansu a lokacin da Sojoji suka kama su.
A cewar Ukume, bayan Sojojin sun kama su ne, sai suka bi gidajensu, inda suka dauko makaman da suke amfani da su wajen kare kansu daga hare haren makiyaya yan bindiga.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
]KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng