Allah ya yi ma Dan uwan shahararren dan wasan Najeriya Rashidi Yakini rasuwa

Allah ya yi ma Dan uwan shahararren dan wasan Najeriya Rashidi Yakini rasuwa

Yan uwan da abokan arziki sun shiga jimamin wani babban rashi da iyalan marigayi shahararren dan wasan kwallo na Super Eagles Rashidi Yekini suka yi, mutuwar kanin tsohon dan wasan, Akeem Yekini.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wani daga cikin shuwagabannin kungiyar kwallon kafa ta jihar Kwara, Alhaji Wasiu Lawal ne ya tabbatar da mutuwar Akeem, a ranar Talata, 8 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro

Lawal ya tabbatar ma majiyar Legit.ng mutuwar ne bayan ya dawo daga ta’aziyyar da ya kai ma iyalan Yekinin a gidansu dake garin Ibadan, inda yace Akeem ya rasu ne a ranar Asabar 5 ga watan Mayu a garin Ijagbo, inda yace an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Allah ya yi ma Dan uwan shahararren dan wasan Najeriya Rashidi Yakini rasuwa
Rashidi Yakini

Majiyarmu ta ruwaito Lawal ya fara kokawa ne game da zazzabin cizon sauro dake damunsa, hadi da ciwon jiki kafin ajali ya cimmasa, inda ya mutu ya bar mata guda biyu, yara biyu da mahaifiyarsa.

Idan za'a tuna a shekarar 2012 ne Rashidi Yekini ya rasu a garin Ibadan bayan yayi fama da matsananciyar rashin lafiya, da har ta yi sanadiyyar tabuwar hankalinsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng