An tsinci gawar wani dan kasar waje a wani Otal da ke Legas

An tsinci gawar wani dan kasar waje a wani Otal da ke Legas

Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Gift Mike ta tana nan a ofishin 'yan sanda masu binciken manyan laifuka (CID) na Yaba da ke Legos akan mutuwar saurayin ta dan kasae Africa ta kudu, Daniel Grant da aka tsinci gawar sa a wani Otal da ke Victoria Island a Legas.

Rahotanni sun ce marigayin ya iso Otal din da ke layin Sinatu Daranijo ne ranar Juma'a da ta gabata tare da sahibarsa Gift. Daga baya masoyan sun tafi wani wajen shakatawa mai suna PAT inda suka ci abinci kuma suka dawo Otal din misalin karfe 1.30 na dare.

An tsinci gawar dan kasar waje a wani Otal da ke Legas
An tsinci gawar dan kasar waje a wani Otal da ke Legas

Da gari ya waye, sai Gift ta sanar da ma'aikatan Otal din cewa saurayin nata ya mutu. Manajan Otal din, Abdul Ismail ya tafi dakin da gawar mamacin yake sannan ya kira jami'an 'yan sanda na Maroko.

KU KARANTA: Tarihi: Ladi Kwali, mace ta daya tilo dake jikin takardar kudin Najeriya

Sai dai bayan isowar 'yan sandan, sun gudanar da bincike inda suke kyautata zaton cewa kashe shi akayi ba shine ya kashe kansa ba.

Kwamishinan Yan sanda na Legas, Imohimi Edgal, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce: "Gift tace sun kwanta barci misalin karfe 1:30 na dare amma ta farka bata ganshi a gado ba, hakan yasa ta duba ban daki sai ta sami gawanshi a sagale kuma ta kira ma'aikatan Otal din.

Masanna kimiyyar bincike sun karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan Yan sandan CID na Yaba, Yetunde Longe, sun ziyarci Otal din kuma sunyi gwaje-gwaje.

Sun kuma gano cewa kafar mamacin tana iya taba kasa duk da cewa yana sagale wanda hakan ke nuna cewa bai kamata ya mutu ba idan kafarsa na taba kasa. An dauke gawar mamacin zuwa dajin ajiye gawa na asibitin gwamnati da ke Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel