Dandalin Kannywood: Ban kara fitowa a matsayin dan daudu a fim - Ado Gwanja
Fitaccen dan fim din Hausar nan a matsana'antar shirya fina-finai ta Kannywood kuma shahararren mawaki watau Ado Gwanja ya tabbatar wa da wakilin majiyar mu cewa yayi bangwana da fitowa a matsayin dan daudu a cikin fina-finan sa.
Ado Gwanja wanda yanzu haka yake daya daga cikin mawakan da tauraruwar sa ke haskawa musamman ma a tsakanin mata da kuma wuraren biki yayi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wakilin majiyar mu ta Premium Times Hausa a satin da ya gabata.
KU KARANTA: Sa'adiyya Gyale na shirin dawowa fim
Legit.ng ta samu cewa fitaccen mawakin yace “A’a yanzu kam na dai na fitowa a fina-finan da zai haska ni a matsayin dan daudu. Zan tsaya a barkwanci na kawai."
Haka zalika Ado Gwanja din ya kuma kara bayar da haske game da sana'ar ta sa ta wakoki inda ya bayyana cewa yana matukar godiya ga masoyan sa sannan yayi musu albishir cewa zai ci gaba zazzago masu sabbin wakoki masu dadi don nishadin su.
Gwanja ya shaida mana cewa yana shirin auracewa nan ba da dadewa ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng