Da akwai yiwuwar Ronaldo ba zai buga wasan su na karshe da Liverpool ba

Da akwai yiwuwar Ronaldo ba zai buga wasan su na karshe da Liverpool ba

- Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce za a dauki hoton idan sawun Cristiano Ronaldo amma kuma akwai yiwu war zai buga wasan karshe na gasar zakarun na Turai da zasu kara da Liverpool

- Dan wasan na Portugal, mai shekara 33, ya samu rauni ne a lokacin da ya ci kwallo a wasan da suka tashi 2-2 da Barcelona

Da akwai yiwuwar Ronaldo ba zai buga wasan su na karshe da Liverpool ba
Da akwai yiwuwar Ronaldo ba zai buga wasan su na karshe da Liverpool ba

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce za a dauki hoton idan sahun Cristiano Ronaldo amma akwai yiwuwar zai buga wasan karshe na gasar zakarun Turai da za su kara da Liverpool.

Dan wasan na Portugal, mai shekara 33, ya samu rauni ne a lokacin da ya ci kwallo a wasan da suka tashi 2-2 da Barcelona.

DUBA WANNAN: Barayin gwamnati: Osinbajo ya bayyana mutane uku da suka saci $3B a mulkin Jonathan

Ronaldo ya cigaba da taka leda har aka tafi hutun rabin lokaci amma sai aka cire shi a lokacin da za a dawo zagaye na biyu.

"Ba ma fargaba akan wasan mu na karshe," kamar yadda kocin na Madrid din Zidane ya ce bayan an tashi daga wasan na ranar Lahadi.

Madrid na kokarin lashe kofin zakarun turan a karo na uku a jere. Za su kara da kulob din Liverpool a wasan karshe a birnin Kiev, na kasar Ukraine a ranar 26 ga watan Mayun wannan shekarar.

Ya kara da cewa "baya jindadi yanzu amma ba wata matsala bace babba - ya dan goce ne a kafa kawai".

Ba zan iya fadar tsawon lokacin da zai dauka ba. Za a dauki hoton wurin a ranar Litinin din nan."

Ronaldo ya zura kwallonsa ta 25 a gasar ta La Liga ta bana a wasan su da Barcelona.

Madrid ce ta uku a tebur, dauke da maki 15 tsakaninta da Barcelona wacce tuni ta lashe gasar.

Tawagar ta Zidane na da sauran wasanni uku kafin su kara da Liverpool a maimaicin irin karawar da suka yi a shekarar 1981, wacce Liverpool ta yi nasara da ci daya mai ban haushi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel