Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas

Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas

- Jami'an hukumar 'yan sanda na (RRS) yankin jihar Legas sun kama wani barawon wayar salula inda yace ya saci sama da wayoyi 1,200 na mazauna jihar ta Legas tunda ya shiga kungiyar masu yankan aljihu shekaru 3 da suka wuce

Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas
Wani barawo yace ya saci wayoyi sama da 1200 a jihar Legas

Jami'an hukumar 'yan sanda na (RRS) yankin jihar Legas sun kama wani barawon wayar salula inda yace ya saci sama da wayoyi 1,200 na mazauna jihar ta Legas tunda ya shiga kungiyar masu yankan aljihu shekaru 3 da suka wuce.

DUBA WANNAN: Falalar Azumi: Wani bincike ya nuna yin azumi na hana tsufa da wuri

Wanda ake zargin, Femi Solomon, dan jihar Ogun an kamashi ne a ranar Alhamis a Iyana Owuro, a birnin Legas, bayan ya saci waya kirar Samsung daga wurin wani mutum a tashar mota.

Solomon dai yace yana sana'ar sayar da gwanjo ne kafin ya shiga sana'ar yankan aljihu. Kamar yanda yace, wani abokin kasuwancin shi mai suna Isma'ila shi ya sashi a hanya.

Yace "Na lura cewa yana zuwa Obalende inda nake siyarda gwanjo tsaf tsaf, da kuma kudi masu yawa. Sai nace mishi ina neman aikin da yafi wanda nake yi. A take ya tabbatar min da cewa zai taimakeni in samu aikin. Sai yace in dinga binshi har in kware.

" Wata shida cif na dinga binshi, muna satar wayoyi 6 zuwa 8 da kuma wallet daga mutane ba tare da sun sani ba. Duk shi yake rikewa amma a karshen kowace rana yana bani Naira dubu 4 zuwa dubu 6."

Ya cigaba: "A watan Augusta 2016, na fara sata ni kadai, banda karfin halin cire waya daga aljihu da farko kuma ban goge ba. Sai na dau salon fita da dare."

" A hasashena, na saci wayoyi sama da 1,200 a tashoshin motoci da kuma cikin motocin haya a cikin birnin Legas. "

Yace hanyoyin da yafi bi sune Ajegunle, Iyana Owuro zuwa Ketu, Ketu zuwa Ojota da Oshodi zuwa mile 2.

"Ina aiki ne ranar Litinin, Talata, Juma'a da Asabar. Ina kuma zuwa wurin casu da dare da kuma guraren holewa."

An samu wayoyi hudu a gurin wanda ake zargin. An maida wanda ake zargi zuwa SCID don cigaba da bincike.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan, SP Chike Oti yace ana cigaba da farautar bata gari a jihar kuma babu wani bata garin da za a kyale.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel