Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo

Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo

- Mata a yankin arewacin kasar Iraki na neman mazajen aure ruwa a jallo

Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo
Duba kaga inda mata suke neman maza ruwa a jallo

Mata a yankin arewacin kasar Iraki na neman mazajen aure ruwa a jallo.

A birni mafi girma na biyu a kasar ta Iraki, yawan mata marasa aure na cigaba da karuwa babu kakkautawa, musamman ma wadanda suka bawa shekaru 20 baya, yayin da mazajen aure suka zamo tamkar dinare a yankin.

DUBA WANNAN: A karo na farko kasar Saudiyya ta fara baiwa mata manyan mukamai

Wannan lamarin wanda ya kunno kai saboda gudun hijarar da mafi yawancin mazajen yankin suka yi zuwa kasashen ketare, hakan yayi matukar tayar wa da matan yankin hankali.

Bincike ya nuna cewar kashi uku ciki hudu na mazan yankin sun bar kasar ga baki daya, don guje wa matsin lamba da haramtacciyar kungiyar DAESH take yi musu.

A yanzu haka dai, matan yankin Mosul na ci gaba da neman mazajen aure ruwa a jallo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel