Harin Birnin Gwari: Rundunar Soji za ta girke Dakarun dindindin a Birnin Gwari – El-Rufai

Harin Birnin Gwari: Rundunar Soji za ta girke Dakarun dindindin a Birnin Gwari – El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna a karkashin gwamna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta jajanta ma al’ummar garin Birnin Gwari, musamman iyalan wadanda aka kashe musu yan uwa a hare haren da yan bindiga ke kaiwa garin.

Premium Times ta ruwaito a ranar Asabar 5 ga watan Mayu ne wasu yan bindiga suka kai sabon hari a kauyen Gwaska dake garin Birnin Gwari da misalin karf 2 na rana, inda suka kashe sama da mutane Arba’in.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Jirgin shugaban kasa ya tashi daga Daura ya nufi babban birnin Tarayya Abuja

Dayake jawabin game da kashe kashen da yaki ci yaki cinyewa, gwamna El-Rufai ta bakin Kaakakinsa ya bayyana damuwarsa game da hare haren, kuma gwamnatin jihar na tuntubar gwamnatin tarayya kan hanyoyi shawo kan lamarin.

Harin Birnin Gwari: Rundunar Soji za ta girke Dakarun dindindin a Birnin Gwari – El-Rufai
Sojoji

“Tattaunawa tsakanin Gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar ta haifar da da mai ido, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar kafa wata bataliyar Sojoji a yankin Birnin Gwari, hakazalika wannan sabon tsari zai kunshi Yansanda, inda babban sufetan Yansanda ya bada umarnin kafa sabuwar runduna, da ofisoshin DPO guda biyu” Inji shi.

Daga karshe Kaakaki Samuel ya tabbatar da cewar tuni hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kaduna ta isa garin Birnin Gwari don tallafa ma wadanda abin ya shafa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel