A karo na farko kasar Saudiyya ta fara baiwa mata manyan mukamai
-
An nada Samar Bint Mazin Salih a matsayin jakadar kasuwancin kasar Saudiyya ta kasar Japan, Samar ta kasance mace ta farko da kasar ta Saudiyya ta fara baiwa mukami mai girma irin wannan.
Ministan kasuwanci da cinikayya na kasar Saudiyya Majid bin Abdullah el Kasabi shine ya tabbatar da hakan, ya bayyana cewar hukumar kasar ta nada Samar Bint Mazin Salih a matsayar jakadar kasuwancin Saudiyya a ofishin jakadancin kasar dake Tokyo babban birnin Japan.
Ma'aikatar ta bayyana cewar anyi hakan domin a kara inganta mata a harkokin kasar.
An bayyana cewar Samar Bint Mazin Salih wacce tayi karatunta na master a jami'ar City University of London a fannin jarida da sadarwa ta taba rike wannan mukamin a ofishin jakadancin Saudiyya dake Italiya.
DUBA WANNAN: Kuda wajen kwadayi yakan mutu: An kama Trump da laifin bawa wata 'yar fim din batsa kudi don ta rufa masa asiri
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng