Ka ci baka ci ba, baka ci ba ka ci: An banka ma Sakatariyar wata karamar hukuma wuta a Bauchi

Ka ci baka ci ba, baka ci ba ka ci: An banka ma Sakatariyar wata karamar hukuma wuta a Bauchi

Matasan jam’iyyar APC da suke ganin ba’yi musu adalci ba a zabukan shuwagabannin jam’iyyar a matakin mazabu da suka gudana a ranar Asabar zuwa Lahadi sun banka ma Sakatariyar jam’iyyar wuta dake karamar hukumar Ningi na jihar Bauchi.

Gidan rediyon muryar Amurka, VOA, Hausa ne ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace matasan zun yi zargin an shanyasu na tsawon awanni ba tare da an gudanar da zaben ba kamar yadda aka shirya ba.

KU KARANTA: Kudi a kashe ta hanya mai kyau: Ronaldo ya baiwa budurwarsa kyautar Zoben naira miliyan 300

Majjiyar Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido yana cewa a bayan jama’a sun jira tun safe har bayan karfe uku na rana, sai wasu shuwagabanni suka yi kokarin yi ma mutane jawabi don tattausasu, hakan ne ya harzuka matasan, inda ba tare da wata wata ba suka cinna ma sakatariyar wuta.

Dayake tabbatar ma majiyarmu faruwar wannan lamari, Daraktan sashen mulki na karamar hukumar, Kabiru Abdullahi Muhammad ya bayyana cewar da kyar suka shawo kan wutar, amma yace wasu sassan sakatariyar ce suka kone, ba duka ba.

Sai dai wani dan jam’iyyar mai suna Ahmed Tijjani Baba Gamawa ya bayyana cewa an bada takardun gudanar da zaben ga yan jam’iyyar, amma rashin bayar dasu akan lokaci ne ya harzuka jama’a, har ta kai ga abinda ya faru ya faru, wanda yayi sanadin rashin gudanar da zaben gaba daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel