Kwarankwatsa ta fado a jihar Taraba, ta kashe mutane biyar tare da raunata Fasto

Kwarankwatsa ta fado a jihar Taraba, ta kashe mutane biyar tare da raunata Fasto

A kalla mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu da yawa suka samu raunuka bayan fadowar kwarankwatsa a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Kwarankwatsar ta lalata gidaje, wurin bauta, ofisoshi, makarantu, da sauran su.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Taraba, ASP David Misal, ya tabbatar d da faruwar lamarin ga manema labarai.

"Tabbas an samu fadowar tsawa mai karfin gaske (kwarankwatsa) da tayi sanadiyar mutuwar mutane hudu bayan da tsawar ta haddasa faduwar karfen sabis a kansu.

Kwarankwatsa ta fado a jihar Taraba, ta kashe mutane biyar tare da raunata Fasto
Kwarankwatsa ta fado a jihar Taraba, ta kashe mutane biyar tare da raunata Fasto

Ya kara da cewar mai yiwuwa adadin mutanen da abin ya shafa ya karu.

Shugaban kungiyar likitoci a jihar Taraba, Dakta Dashe Dasogot, ya tabbatar wa da jaridar Daily Trust cewar an kawo gawar mutane biyar asibitin kwararru na Jalingo bayan fadowar kwarankwatsar.

Dasogot ya nunawa manema labarai wasu bishiyoyi da gine-gine a cikin asibitin da faduwar karfen ta shafa.

DUBA WANNAN: Gaba da gaban ta: ‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa sun ji maza, kalli hotunan su

Wata shaidar gani da ido, Uwargida Henrietta Anthony, ta bayyana cewar uku daga cikin 'yan uwan ta, Aisha Useni, Felicia Istifanus da Istiah James, na daga cikin mutane hudun da suka mutu.

Kazalika fadowar tsawar ta shafi wani ginin Coci tare da jikkata wasu mutane bakwai da wani Fasto, Ravaran John Jerome, dake cikin ta lokacin da ta rushe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel