Yanzu-yanzu: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kungiyar gwamnonin APC na kasa
- Shugaba Muhammadu Buhari na wata ganawa da shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC, Rochas Okorocha, a birnin Daura
- Tattaunawar da har ya zuwa yanzu ba'a bayyana makasudinta ba, amma sai dai na kyautata zaton ziyarar na da nasaba da zaben 2019
- Tun dai kafin tafiyar Muhammadu Buhari kasar Amurka gwamnonin APC suka nuna goyon bayan su ga takarar sa
Da yammacin yau Lahadi ne shugaban kungiyar gwamnonin APC na kasa kuma gwamnan jihar Imo, Rochas Okorochas, ya kaiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a mahaifarsa dake Daura.
Tattaunawar da har ya zuwa yanzu ba'a bayyana makasudinta ba, amma sai dai na kyautata zaton ziyarar na da nasaba da zaben da ake shirye-shiryen gudanarwa na shugabancin jam'iyyar na kasa da kuma batun sake tsayawa takarar shugaban a 2019.
KU KARANTA: Atisayen AYEM AKPATUMA: Duba hotunan aiyukan jin kai da dakarun soji keyi a jihar Taraba
Tun dai kafin tafiyar Muhammadu Buhari kasar Amurka gwamnonin APC suka nuna goyon bayan matsayin da ya zaba na a gudanar da zaben shuwagabannin jam'iyyar maimakon karin wa'adi da akai musu na shekara guda.
Muhammadu Buhari bayan dawowarsa daga kasar Amurkan dai ya wuce mahaifarsa ne domin yin hutun karshen mako kafin daga bisani ya koma Abuja gobe Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng