2019: Atiku Abubakar na shirin doke Shugaban kasa Buhari

2019: Atiku Abubakar na shirin doke Shugaban kasa Buhari

- Wasu Matasan Najeriya su na goyon bayan Atiku Abubakar

- Matasan sun ce babu fa wanda ya dace da Najeriya irin Atiku

- Shugaban Tafiyar yace Atiku ya cancanci ya rike kasar a 2019

Maganar yakin neman zaben tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yayi nisa bayan da wasu Matasa su ka nuna cewa za su fito kwan-su da kwarkwatar su domin mara masa baya da kira a zabe sa a Najeriya.

2019: Atiku Abubakar na shirin doke Shugaban kasa Buhari
Wazirin Adamawa Atiku Abubakar na kokarin doke Buhari

Yayin da zaben 2019 ya karaso mun samu labari cewa Atiku Abubakar ya bazama wajen neman kujerar Shugaban kasa inda wasu Matasa su kayi masa alkawarin mutane kalla miliyan da za su yi tattaki domin nuna goyon-baya.

KU KARANTA: Ministocin Shugaba Buhari da su kayi kusufi a Gwamnati

Kungiyar Matsan da Kwamared Adegboyega Adeleke ya kaddamar da wani shiri na #Unstoppable2019 a Jihar Kaduna domin ganin tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya karbe kujera daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

Matasan sun bayyana cewa Atiku yana cikin ‘Yan takarar da za su iya gyara kasar nan kuma ya kware a kan lamarin siyasa a harkar tattalin arziki. Adegboyega Adeleke ya yabawa kokarin Atiku wajen dawowar mulkin farar hula a 1999.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana babban dalilin sake tsayawa takarar sa. Shugaban kasar yace tsantsagoron kawo gyara a Najeriya ya sa ya ke neman zaracewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng