Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci taron jam'iyyar APC a garin Daura
Mun samu rahoton cewa a yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya halarci taron jam'iyyar sa ta APC a mazabar sa ta Sarkin Yara A dake mahaifar sa ta garin Daura a Jihar Kastina.
Bayan abin da bai wuci sa'o'i 48 ba da dawowar shugaba Buhari daga ziyarar aiki a kasar Amurka inda ya gana da shugaba Donald Trump, ya kuma garzaya mahaifar sa ta Daura domin biyan bukata ta jam'iyyar sa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Buhari ya garzaya zuwa garin na Daura domin halartar wannan taro na jam'iyyar sa ta APC a mazabar sa.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a yau ne ake gudanar da taron jam'iyyar APC a kowace mazaba dake fadin kasar nan kamar yadda jam'iyyar ta shirya gudanarwa a ranar Asabar wadda ta yi daidai da 5 ga watan Mayun 2018.
KARANTA KUMA: Dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke ci gaba da amfani da Motocin da ya gada na Jonathan
Rahotanni kuma sun bayyana cewa, ana sa ran shugaba Buhari zai ziyarci jihar Jigawa a ranar Litinin ta mako mai gabatowa domin kaddamar da wasu sabbin aikace-aikace da gwamnatin jihar ta aiwatar karkashin jagorancin gwamna Muhammad Badaru.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng