Tarihi: Ladi Kwali, mace ta daya tilo dake jikin takardar kudin Najeriya
'Yan Najeriya da dama basu san labarin matar da aka sanya hoton ta a bayan naira 20 da suke kashewa yau da kullum ba. Matar da hoton ta ke bayan naira 20 na kudin Najeriya wata fitaciyar mai sana'ar kera tukwane ce mai suna Ladi Kwali.
An haifi Ladi Kwali ne a wani kauye mai suna Kwali, wanda ke yankin Gwari da a yanzu yake karkashin birnin tarayya Abuja, dama dai sana'ar kera tukwane shahareren sana'a ne ga matan yankin.
Kwali ta taso ne a gidansu inda mata sana'ar kirar tukwane don su sami abin da zasu tallafawa kansu kuma itama ta koya sana'ar wajen kanwar mahaifiyarta tun tana karamar yarinya.
A cewar kanin ta mai suna Mallam Mekaniki Kyebese: "Tun lokacin da take karama, tana da matukar hazaka wajen kirar tukwane da wasu abubuwan, galibi ma mutane kan saye tukwanenta tun kafin ta kai kasuwa.
Da taimakon wani dan kasar Ingila mai sha'awar daukan hotunan tukwane, Michael Cardew, Kwali tayi suna a duniya a shekarun 1950s. Daga baya an nada Cardew a matsayin jami'i mai kula da kera tukwane a ma'aikatan kasuwanci da masana'antu a shekarar 1951 inda ya kafa makarantar koyar da kera tukwane na Abuja a tare da Kwali a 1952 inda suka kwashe shekaru 15 suna koyar da kera tukwane.
KU KARANTA: Boko Haram za su mika wuya - Aisha Wakil
Tukwanen da Kwali ke karewa sunyi suna saboda kyawun su da inganci hakan yasa Sarkin Abuja a wannan lokacin, Suleiman Barau ya saya tukwane da yawa daga wurinta don kayata fadar sa.
Daga bisan Kwali da Cardew sun tafi ziyara a kasar Amurka da Landan inda aka gabatar da ayyukan ta wurare da dama kuma mutane na ta sha'awa da mamakin irin baiwar da take dashi.
Ga wasu daga cikin lambobin yaba da karamawa da ta samu:
1) A shekarar 1962 an karrama ta da MBE (Member of the Order of the British Empire), a kuma 1977 jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ta karrama ta da digirin girmamawa na Dacta, (Honorary Doctorate).
2) Gwamnatin Najeriya ta karramata da lambar yabo mafi girma a Najeriya na ilimi wato 'Nigerian National Order of Merit Award'
3) A shekarar 1981, ta samu lambar yabo na (OON) wato Officer of the Order if the Niger.
4) A sanya sunanta a wani layi a babban birnin tarayya Abuja wato Ladi Kwali Street.
5) An canja sunan makarantar koyar da kera tukwanen na Abuja zuwa Ladi Kwali Pottery.
6) An sanya hoton ta a bayan naira 20 na kudin Najeriya, itace mace na farko da aka sanya hoton ta a kudin Najeriya.
Bayan Cardew ya rasu a shekarar 1983, Ladi Kwali ta rasu a ranar 12 ga watan Augusta tana da shekaru 59 a duniya a garin Minna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng