Anyi dauki ba dadi da jami'an NDLEA yayin da suka je kama wani dillalin miyagun kwayoyi
Jami'an hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun harbi a kalla mutane hudu ne ciki har da dalibin makarantar framari da kuma wani mai gadin makarantar sakandire na Dolphin High School da ke Legas.
Dalibin wanda a yanzu ba'a bayyana sunanan sa ba ya riga mu gidan gaskiya saboda raunin da harsashin tayi masa yayinda shi kuma mai gadin makaranta, Godwin Nsidieti, ya rasa idon sa na hagu saboda harsashin da ya ratsa idon.
Sauran mutane biyu da suka sami rauni sun hada da wani ma'aikacin gwamnati mazaunin Igunu street da kuma Nurudeen Animashaun.
KU KARANTA: Fitataccen farfesa ya cacaki masu fakewa da rashin lafiya bayan an kama su da almundahana
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami'an NDLEA sun kai samame ne a Topa street misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata 17 ga watan Afrilun don kama wani dilalin miyagun kwayoyi inda suka ajiye motarsu a kusa da marantar sakandiren.
Amma a yayin da suke gudanar da bincike a Patey, wani layi da ke makwabtaka da inda suka je, wasu matasa sun bijiro musu inda sukayi kokarin fatatakar su. Hakan yasa jami'an na NDLEA suka fara ruwan harsasai inda har guda daya ta harbi dalibin da ke tafiya makaranta.
Shi kuma mai gadin ya fito ne daga makarantar don ya duba abin da ke faruwa amma sai akayi rashin sa'a wata harsashi ta same shi a ido. Daga bisan jami'an na NDLEA sunyi tafiyarsa yayinda aka garzaya da wadanda suka harbi zuwa asibiti.
A wanda abin ya faru a idonsa, wanda ya ce sunansa Raphael ya ce jami'an NDLEA din sun kuma tafi da wani gurgu bayan sun gama samamen. Ya ce kafin zuwan jami'an na NDLEA, Yan sandan yaki da masu fashi da makami sun kawo samame a unguwar.
Kakakin Yan sanda na Legas, SP Chike Oti ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace hukumar Yan sandan ta rubuta wasika ga NDLEA inda suka bukaci a turo musu jami'an da suka kai wannan samamen don su amsa tambayoyi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng